Afrika ta Kudu ce zata dauki bakuncin kwallon matasa

soccer city
Image caption Bukin gasar cin kofin duniya a 2010

Afrika ta Kudu ce zata dauki bakuncin gasar cin kofin kwallon matasan Afrika 'yan kasada shekaru 20 wanda a baya aka shirya yi a Libya.

Gasar ya kamata a fara ne a ranar 18 ga watan Maris a Tripoli amma sai aka dakatar saboda tashin hankali a kasar.

Hukumar dake kula da kwallon Afrika Caf ta ce a yanzu za a fara gasar ce daga ranar 17 ga watan Afrilu zuwa biyu ga watan Mayu.

Shugaban Caf Issa Hayatou ya ce Afrika ta Kudu wacce a baya ba zata buga gasar be, a yanzu ta maye gurbin Libya a rukuni na farko.

Kenan Afrika ta Kudun na rukuni guda da Mali da Masar da kuma Lesotho.

Sai kuma rukuni na biyu inda Ghana ke tare da Najeriya da Kamaru da kuma Gambia.

Kasashe biyun farko daga kowane rukuni zasu tsallake zuwa gasar cin kofin duniya na matasa a Columbia watan Yuli.