An yiwa Messi da Xavi gwajin haramtattun kwayoyi

messi Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Gwazayen Barcelona:Messi, Iniesta da Xavi

'Yan kwallon Barcelona goma ciki har da Lionel Messi da Xavi Hernandez aka yiwa gwaji akan shan haramtattun kwayoyi masu kara kuzari.

Gwajin dai na cikin tsarin hukumar dake kula da kwallon Turai wato Uefa don tabbatar da cewa 'yan kwallo basa shan kwayoyin da aka haramta.

A ranar Alhamis ne likitocin Uefa suka halarcin sansannin horon Barca akaro na biyu cikin shekaru uku.

Wannan gwajin yazo ne 'yan kwanaki bayan da wani gidan rediyon kasar Spaniya ya bada labarin cewar babbar abokiyar hammayar Barcelona wato Real Madrid na kurarin cewa, ba dai dai bane likitocin da ake tababa akan aikinsu,su dinga yin aiki tare da Barca.

Sai dai Barcelona tayi barazanar daukar hukunci na shari'a akan gidan rediyon.

'Yan wasan da aka gwada jininsu,sun hada da Gerrard Pique da David Villa da Jefferen Suarez da Jose Manuel Pinto.

Sauran sune Andre Iniesta da Victor Valdes da Javier Mascherano da kuma Ibrahim Afellay.