Zuwan Torres bai firgitani ba-Drogba

drogba
Image caption Didier Drogba

Didier Drogba ya karyata cewar zuwan Fernando Torres a Chelsea ya kawo mashi fargaba.

Kaptin din Ivory Coast din ya ce yana jin dadin taka leda a Stamford Bridge.

An yita jita-jita akan makomar Drogba tunda aka siyo Torres akan makudan kudade.

Dan kwallon mai shekaru 33, a yanzu ba kowanne wasa ake farawa dashi, sabannin yadda lamarin yake a shekarun baya.

Drogba ya kasa zira kwallo a cikin wasanni tara da suka wuce, kuma tun zuwan Torres basu fahimci juna ba a gaban Chelsea.

A halin yanzu saura watanni 18 kwangilar Drogba ta kare, kuma baya batun sabunta yarjejeniyar.