Watakila Ferdinand ba zai kara taka leda a kakar wasa ta bana

rio
Image caption Rio Ferdinand

Dan kwallon Manchester United Rio Ferdinand watakila ba zai kara taka leda ba a kakar wasa ta bana saboda rauni a kafarshi.

Kaptin din Ingilan yaji raunin ne lokacin horo kafin wasan United da Wolves a ranar biyar ga watan Fabarairu.

Kocin United Sir Alex Feguson ya ce "bama tunanin zai murmure a nan kusa, amma watakila ya buga a karshen kakar wasa ta bana".

Har wa yau United ta samu wani mummunar labari akan John O'Shea saboda zai yi jinyar kafadarshi na makwanni biyar.

Shima Nemanja Vidic yana jinyar rauni a kafarshi kuma ba zai buga wasansu da Bolton ba, abinda kuma ke nuna cewar a yanzu 'yan kwallon baya ne kadai suka rage wato-Fabio, Chris Smalling, Wes Brown da kuma Patrice Evra.