Mun zaku mu fafata da Ingila a Wembley-Muntari

ghana Hakkin mallakar hoto b
Image caption 'Yan Sunderland:John Mensah da Asamoah Gyan da kuma Sulley Muntari

Dan kwallon Ghana Sulley Muntari ya ce sauran abokan wasanshi John Mensah da Asamoah Gyan sun zaku a buga wasan sada zumunci tsakaninsu da Ingila a Wembley a ranar 29 ga watan Maris.

'Yan kwallon Sunderland din na cikin tawagar Black Stars da zasu buga wasan, inda masu goyon bayan Ghana dubu ashirin zasu halarta.

Muntari yace "muna son mu buga, a Wembley ne, kuma zamu fafata da daya daga cikin manyan kasashe a fagen kwallon duniya".

Muntari ya kara da cewar:"muna dade muna jiran wannan wasan, kuma mutane a Ghana sun zaku suma su ganmu tare da Ingila".

Muntari ya koma Sunderland a matsayin aro daga Inter Milan shekaru biyu da rabi da barin gasar premier.

Dan shekaru 26 ya lashe gasar cin kofin FA tare da Portsmouth kafin ya koma Inter Milan akan pan miliyan 12.7, inda ya daga kofin gasar zakarun Turai a can Italiya.