FIFA: Bin Hammam zai fafata da Blatter

Muhammad Bin Hammam
Image caption Bin Hammam ya sha alwashin kawo sauyi a FIFA

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Asia Muhammad Bin Hammam, ya ce zai yi takara da Sepp Blatter a zaben shugabancin FIFA da za a yi a watan Yuni.

A wani jawabi da ya yi na mintina 17, Bin Hammam ya yi alkawarin fadada kwamitin zartarwa na FIFA da kuma arzikinta.

"Sauyi ya zama wajibi, kuma ana bukatarsa," a cewar Bin Hammam, wanda zai maida hankali kan gaskiya da kuma amfani da fasahar zamani.

Blatter na neman a sake zabarsa ne a karo na hudu.

Bin Hammam ya ce damarsa ta zamowa shugaban FIFA na farko daga nahiyar Asia na da karfin gaske.

"Bayan tattaunawa da kuma tunani, na ga ya dace na shiga a fafata da ni a zaben na watan Yuni. Ina kuma da goyon bayan kwamitin zartarwa na Hukumar kwallon kafa ta Asia," a cewar Bin Hammam.