La Liga:Real Madrid da Barcelona sun haskaka

benzema
Image caption Karim Benzema na Real Madrid

Real Madrid ta haskaka a karshen mako inda ta doke Atletico Madrid daci biyu da daya, a yayinda itama abokiyar hammayarta Barcelona ta samu nasara ana ta karawan.

Tawagar Jose Mourinho sun nunawa makabtasun cewar ruwa ba tsaran kwando bane inda Karima Benzema da Samu Khedira suka zira kwallayen.

Sergio Aguero ne ya farkewa Athletico kwallo daya.

Can a filin Nou Camp kuwa Barcelona ta cigaba da samun nasara a duka wasanninta, inda kawo yanzu ta buga wasa 27 ba tare da an doke ta ba.

Barca ta casa Gatefe ne daci biyu da daya, inda Dani Alves da Bojan suka ciwa zakarun Spain din kwallaye biyu.

Bayan karawa a wasanni 29, a yanzu Barcelona na da maki 78 sai kuma Real Madrid wacce ke ta biyu da maki 73.