Chelsea ta casa Man City, ta zama ta uku akan tebur

luiz Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption David Luiz

Chelsea ta casa Manchester City daci biyu da nema don maye gurbin na uku akan teburin gasar premier ta Ingila.

Koda yake Carlos Tevez bai buga wasan ba amma Yaya Toure ya kai harin cin kwallo sai golan Chelsea Peter Cech ya kabe ta.

'Yan Brazil David Luis da Ramires sune suka ciwa Chelsea kwallayenta biyu.

Sakamakon sauran karawar da aka yi a gasar premier:

*Sunderland 0 - 2 Liverpool *Tottenham Hotspur 0 -0 West Ham United *Aston Villa 0 - 1 Wolverhampton *Blackburn Rovers 2 - 2 Blackpool *Manchester United 1 - 0 Bolton Wanderers *Stoke City 4 - 0 Newcastle United *West Bromwich … 2 - 2 Arsenal *Wigan Athletic 2 - 1 Birmingham City *Everton 2 - 1 Fulham