Masar ta gayyaci Aboutreika don karawa da Afrika ta Kudu

abutrika
Image caption Muhammed Aboutrika

Kocin Masar Hassan Shehata ya kira tara daga cikin tawagar 'yan kwallon kasar da suka lashe gasar cin kofin Afrika a bara, don fafatawa da Afrika ta Kudu a ranar 26 ga watan Maris.

Sannan kuma an kara su da Mohamed 'Magician' Aboutreika na Ahly wanda bai je Angola ba saboda rauni.

Shima Mahmoud 'Shikabala' Abdelrazek na Zamalek ya samu shiga.

Gola Essam al-Hadary, masu buga baya Ahmed Fathi, Wael Gomaa, Sayed Moawad da Ahmed al-Mohamady, 'yan tsakiya Hossam Ghaly da Hosny Abd Rabou da kuma Mohamed Zidan.

Mohamed 'Geddo' Nagy,wanda a gasar cin kofin Afrika a Angola ake sakoshi bayan hutun rabin lokaci yana daga cikin wadanda ake saran zasu fuskanci Bafana Bafana.

A halin yanzu a rukunin G, Afrika ta Kudu ta dara Masar da maki uku.