An maidoda Terry a matsayin kaptin din Ingila

terry Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption John Terry

An maido da dan kwallon Chelsea John Terry a matsayin kaptin din tawagar 'yan kwallon Ingila.

Kafin kocin Ingila Fabio Capello ya sanarda haka, rahotanni a baya sun nuna cewar mai horadda 'yan kwallon zai dauki matakin.

A bara ne aka cire Terry a matsayin kaptin aka baiwa Rio Ferdinand bayan da aka samu rahotannin cewar, Terry yana neman tsohuwar budurwar Wayne Bridge.

Amma Capello ya ce"bayan horo na shekara guda,Terry zai kara zama kaptin na dun dun dun,saboda labadtarwa ta shekara guda ta isa".

A yanzu Terry ya maye gurbin dan kwallon United Ferdinand wanda rahotanni suka bayyana cewar bai ji dadin tunbukeshi ba a matsayin kaptin.

A halin yanzu Ferdinand na fama da rauni, amma Capello na shirin tattaunawa da shi a filin Old Trafford don ya bayyana mashi dalilan da suka sanya ya cire shi daga mukamin.