Zan gudanar da sauye-sauye a Fifa-Bin Hammam

hammam Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mohammed Bin Hammam

Dan takarar shugabancin Fifa Mohammed Bin Hammam ya ce idan aka zabeshi, zai gyara tsarin yadda ake zaben kasashen da zasu dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a nan gaba.

Bin Hammam ya ce babu cin hanci da rashawa a Fifa amma ya kamata a daina boye-boye akan yadda ake gudanar da hukumar.

Yace"ya kamata mu fayyace yadda ake daukar hukunci, saboda hukunce-hukuncenmu na shafar miliyoyin mutane.

Bin Hammam ya kara da cewar"mu na mutane ne,muna aiki ne a madadin jama'a."

Shugaban Fifa Sepp Blatter ya fuskanci kakkausar suka a watan Disamba, bayan an zabi Rasha da Qatar su dauki bakuncin gasar cin kofin duniya na 2018 da kuma na 2022.

A ranar 31 ga watan Mayu ne za ayi zaben sabon shugaba na Fifa a birnin Zurich.

Blatter mai shekaru 75 ya dare kan kujerar shugabancin Fifa tun a watan Yuni na shekarar 1998, kuma ba a kara kalubalantarshi ba tun shekara ta 2002 lokacin daya doke shugaban hukumar kwallon Afrika wato Caf Issa Hayatou.