An canza inda za a buga wasan Ivory Coast dana Libya

drogba Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kaptin din Ivory Coast Didier Drogba

An sauya inda za a gudanar da wasan Ivory Coast da Libya na neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika a 2012 zuwa wata kasar daban saboda tashin hankalin dake gudana a kasashen biyu.

A yanzu dai Ivory Coast za ta fafata da Benin a kasar Ghana , ita kuma Libya za ta hadu da Comoros a Mali.

Zaman dar-dar da ake yi a Ivory Coast ya tilasta daga wasan ranar Lahadi daga Abidjan zuwa Accra.

Shugaban hukumar dake kula da kwallon Ghana-GFA Kwesi Nyantakyi ya ce"Ivory Coast za ta buga wasanta da Benin a Accra, saboda dalilai na tsaro".

Ivory Coast a yanzu tana kokarin kara tazara a rukunin H saboda tana da maki shida cikin karawa biyu.

Wasan Libya da Comoros za a buga ne a Bamako a ranar Lahadi saboda fada tsakanin 'yan tawaye da kuma shugaba Muammar Gadhafi.