Shugaba Bongo ya ce Gabon ta shiryawa 2012

bongo
Image caption Shugaba Ali Bongo na Gabon

Shugaban Gabon Ali Bongo ya ce kasarshi ta shirya daukar bakuncin gasar cin kofin kasashen Afrika a shekara ta 2012, duk da irin damuwar da ake da ita wajen shirye-shiryen da kasar keyi.

Bongo ya ce wasu daga cikin tsare-tsaren na tafiya lami lafiya, amma wasu na tafiyar hawainiya.

Shugaban wanda ya kai ziyara London ya ce"idan na koma gida a makon daya gabata, zan kai ziyarar gani da ido a duka wajajen da za a gudanar da gasar".

Bongo ya kara da cewar za a kamalla komai kafin ranar 21 ga watan Junairun badi.

Daga ranar 21 ga watan Junairu zuwa 12 ga watan Fabarairu ne za ayi gasar cin kofin kasashen Afrika a kasashen Gabon da Equitorial Guinea".