Akwai rarrabuwar kawuna a Ingila kai na-Terry

terry
Image caption Capello na baiwa Terry shawara

John Terry ya amince akwai rarrabuwar kawuna akan batun maido mashi da kambum kaptin din Ingila.

An cire Terry ne sakamakon yadda yake tafiyar da rayuwarshi watanni 13 da suka wuce, amma sai aka kara dawo dashi ya maye gurbin Rio Ferdinand.

Terry yace"na son ba kowa bane ke sha'awa na, amma a yanzu nayi hankali".

Rahotanni sun nuna cewar Ferdinand ya fusata da matakin na kocin Ingila Fabio Capello na cire shi ya maidawa Terry shugabancin.

Terry ya kara da cewar Rio ya kira shi ya tayashi murna,abinda ke nuna halin dattaku.

A watan Fabarairun 2010 ne aka cire Terry a matsayin kaptin aka baiwa Ferdinand, bayan rahotanni dake nuna cewar yana mu'amala da tsohuwar buduwar Wayne Bridge.