Bana son in bar Leicester City-Yakubu

Yakubu Aiyegbeni
Image caption Yakubu Aiyegbeni

Dan kwallon Leicester Yakubu Aiyegbeni wanda aka karbo shi aro daga Everton ya ce a karshen kakar wasa ta bana , yanason zama dun-dun-dun a sabon kulob din.

Dan shekaru 28, ya koma Leicester ne a watan Junairu kuma ya buga wasanni masu mahimmanci wadanda zasu taimakawa kungiyar ta buga wasan kifa daya kwala don komawa gasar premier.

Ya shaidawa BBC cewar"Ina son in cigaba da zama anan.Ina son in kasance anan tunda kungiyar na son komawa gasar premier".

Yakubu ya kara da cewar"na dauki babban hukunci akaina na barin Everton, saboda inason in cigaba da taka leda akan kari".