Adebayor ya karyata komawa Togo amma Keshi ya koma

togo
Image caption Ana son Emmanuel Adebayor a Togo

Emmanuel Adebayor ya karyata cewar zai koma takawa Togo kwallo a wasanta na ranar Asabar tsakaninta da Malawi.

Shugaban hukumar kwallon Togo Gabriel Ameyi shine ya bayyanawa manema labarai cewar dan kwallon Real Madrid din a wannan makon zai koma bugawa kasar kwallo.

Adebayor ya shaidawa BBC cewar "ban dauki alkawarin komawa cikin tawagar a wasan Togo da Malawi ba".

Dan kwallon Real Madrid Adebayor ya daina bugawa kasar kwallo ne bayan harin bindiga da aka kaiwa motar dake dauke da tawagar 'yan kwallon Togo lokacin gasar cin kofin Afrika a shekara ta 2010 inda aka kashe mutane biyu.

Sai dai dan Najeriya Stephen Keshi a halin yanzu yana Togo don maye gurbin dan Faransa Thierry Froger a matsayin mai horradda 'yan kwallon kasar.

Keshi a baya ya jagoranci Togo a shekara ta 2007 da kuma tsakanin 2004-2006,inda ya tsallakar da kasar zuwa gasar cin kofin duniya a 2006.