Boateng ya janye daga tawagar Ghana saboda rauni

Kevin Prince Boateng Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kevin Prince Boateng

Rauni ya tilastawa Kevin Prince Boateng fasa shiga cikin tawagar Ghana da zata fafata da Congo a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin kasashen Afrika na badi.

Dan wasan AC Milan din har wa yau ba zai buga wasan sada zumuncin Black Stars da Ingila a ranar Talata da za a buga a Wembley.

Amma dai shi kuwa Sulley Muntari yana saran zai murmure daga raunin da yayi fama dashi, don ya buga wasansu da Congo da kuma na Ingila.

Wani dan wasa da tabbas ba zai bugawa kasarshi ba shine Vincent Enyeama na Najeriya wanda aka maye gurbinshi da Sunday Rotimi a cikin tawagar Super Eagles da Samson Siasia ya gayyata.

Can ma a Afrika ta Kudu sabon kaptin din Bafana Bafana Steven Pienaar wanda ya maye gurbin Aaron Mokoena akwai tababa akan bugawarshi saboda jimuwa da yayi a wasan daya bugawa Spurs a Ingila.

Shima dan kwallon Algeria Madjid Bougherra akwai shakku akan koshin lafiyarshi har ya buga wasansu da Morocco.