Uefa: Mourinho ya jinjinawa Tottenham

mourinho Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jose Mourinho

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya jinjinawa Tottenham akan namijin kokarin data yi a gasar zakarun Turai.

Real zata kara da Spurs a zagayen gabda na kusada karshe na bugu biyun da za ayi a ranakun biyar da goma sha uku ga watan Afrilu.

Mourinho ya shaidawa BBC cewar"Tottenham tayi abu me kyau, kuma suna da hujjar yin murna akai".

Ya bayyana haka ne a London cikin hutu na mako guda da yake yi saboda zasu a buga kwallon kasashe,kuma tsohon kocin Chelsea ya ce abune me yiwuwa tawagar 'yan kwallon Harry Redknapp su lashe gasar.

Mourinho ya kuma bayyana cewar ya ji dadi da ba a hadasu da tsohuwar kungiyar daya jagoranta wato Chelsea da Inter Milan.