Rauni zai hana Bale buga wasan Wales da Ingila

bale Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gareth Bale

Gareth Bale ba zai buga wasan Wale tsakaninta da Ingila, na neman gurbin shiga gasar cin kofin kwallon kasashen Turai da za ayi a badi, saboda rauni a kafadarshi.

Hukumar kwallon Wales a wata sanarwa ta ce raunin da Bale ya samu, kafin ya hade da tawagar Wales ne.

Dan kwallon Tottenham din mai shekaru 21 bai shiga cikin horo ba a ranar laraba.

Sanarwar tace"saboda matsala a kafadarshi, Gareth Bale ya janye daga tawagar Wales da zata kara da Ingila".

A kwananan ne Bale ya murmure, bayan ya shafe makwanni shida baya takawa Spurs kwallo saboda ciwon baya.