Ana takaddama akan La Liga saboda harajin talabijin

messi
Image caption Messi da Ronaldo zakarun La Liga

Za a samu karin makwanni uku kafin kamalla gasar La Liga ta Spain bisa yadda aka tsara a baya, saboda dage wasannin gasar saboda takaddama akan harajin kudin kallo na talabijin.

Kulob kulob na bukatar a sauya dokar data ce anuna akalla wasa guda kyauta a gidajen talabijin a kasar.

A ranar Laraba hukumar kwallon Spaniya-LFP ta ce ba a samu wani cigaba ba a tattaunawa tsakaninsu da gwamnatin Spaniya wajen warware matsalar.

Sun ce , a halin da ake ciki a yanzu, za a buga wasanni a ranar 12 ga watan Yuni.

Rahotanni daga Spaniya wasu kungiyoyi sun kai kara kotu don a cigaba da fafatawa a gasar, jaridar Marca ta ce Sevilla, Villarreal, Athletic Bilbao, Real Sociedad, Espanyol da kuma Zaragoza sun bukaci kotu ta bada umurnin a cigaba da gasar.