An nada Beckham kyaftin a LA Galaxy

David Beckham
Image caption David Beckham ya shafe shekaru uku a LA Galaxy

A karon farko cikin shekaru uku an nada David Beckham a matsayin kyaftin din kungiyar Los Angeles Galaxy ta Amurka na wucin gadi.

Tsohon dan wasan na Ingila mai shekaru 35, ya taba rike mukamin a 2007, amma daga baya Landon Donovan - wanda ke halartar horo domin bugawa kasarshi wasa - ya karbe matsayin tun bayan zuwansa.

Donovan ya nuna shakku kan yadda Beckham ya dauki kulob din a shekarar 2009, sannan kuma magoya baya suka yi masa ihu.

"Zan yi alfahari sosai idan na sanya kyaftin," a cewar Beckham.

"Ba zai sauya yadda nake taka leda ba. Abin alfahari ne, amma ana bukatar jagora fiye da daya a filin wasa".