Barry zai jagoranci Ingila a wasan Ghana

Gareth Barry
Image caption Gareth Barry yana taka leda sosai a Manchester City

Kocin Ingila Fabio Capello, ya bayyana dan wasan Manchester City Gareth Barry a matsayin wanda zai jagoranci Ingila a wasan sada zumuntar da za su yi da Ghana a Wembley.

Barry, mai shekaru 30, zai jagoranci wata sabuwar tawaga ce daban da wacce ta doke Wales da ci 2-0 a ranar Asabar.

Capello ya mayar da John Terry a matsayin kyaftin din England sannan ya bayyana dalilin da ya sa ya tattauna da Steven Gerrard kadai, amma bai yi da Rio Ferdinand ba.

"Rio shi ne kyaftin, don haka wajibi ne na gana da shi. Steve mataimaki ne kawai," a cewarsa.

Capello, wanda ya bayyana cewa ya yi kuskure wajen zabar kyaftin a makon da ya gabata, ya kara da cewa: "Ina fatan yin magana da Rio a mako mai zuwa."