Brazil ta lallasa Scotland da ci 2-0

Brazil Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Brazil na kokarin farfadowa daga mummunar rawar da ta taka a Afrika ta Kudu

Matashin Brazil Neymar ya zira kwallaye biyu a wasan sada zumuntar da Brazil ta doke Scotland da ci biyu da nema a filin wasa na Emirates.

Jadson da Leandro Damiao ma sun kai munanen hare-hare kafin Neymar ya zira kwallon farko gab da tafiya hutun rabin klokaci.

Dan wasan na Santos ya zira kwallo ta biyu ne ta bugun fanareti bayan da Charlie Adam ya kada da shi.

'Yan wasan Scotland sun kasa taka rawar gani a wasan, harin da Barry Bannan ya kai shi ne daya tilo da suka kai.