Scotland ta musanta zargin Neymar

Matashin Brazil Neymar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Neymar ne ya zira kwallaye biyun da Brazil ta doke Scotland

Hukumar kula da kwallon kafa ta Scotland ta musanta zargin da dan wasan Brazil Neymar ya yi, cewa magoya bayan scotland sun yi masa kalaman wariyar launin fata.

An jefa ayaba a cikin filin wasa na Emirates bayan da Brazil ta zira kwallo ta biyu, sannan Neymar ya yi zargin banbancin launin fata. Wata sanarwa da Hukumar SFA, ta fitar ta ce: " Hukumar kwallon Scotland ta yi watsi da zargin da Neymar ya yi, cewa an nuna masa banbancin launin fata."

Ta ce babu wata hujja, amma magoya bayan Scotland sun tabbatar da cewa sun yi masa ihu "kan rashin da'ar da ya nuna."

Kwamandan 'yan sanda a filin wasan Mark Sheeran ya ce: "Dabi'ar magoya bayan Scotland na da kyau sosai. Babu wani abu da ya faru a filin wasan kwata-kwata."