Tsohon kyaftin din Ghana ya fusata da Ingila

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Stephen Appiah

Tsohon kyaftin din Ghana Stephen Appiah ya ce kocin Ingila Fabio Capello bai kyauta ba da bai sanya manyan wasan kasar da za su kara da Ghana ba.

Kocin Ingila Capello ya kare matakin ajiye manyan 'yan wasan shi biyar a wasan sada zumuncin da Ingila za ta kara da Ghana a filin Wembley.

John Terry da Ashley Cole da Frank Lampard da Wayne Rooney da kuma Michael Dawson ba za su taka leda ba a wasan bayan sun buga a wasan da Ingila ta doke Wales a ranar asabar.

Appiah, mai shekarun haihuwa 30, ya shaidawa BBC cewa Ingila bata daukin wasan da mahimmanci ba.

Ghana ta siyarda tikiti 21,000 na shiga kalllon wasan.