Dan wasan Man City Boateng ya samu rauni

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Jerome Boateng a wasan da City ta buga da Ingila

Za'a yiwa dan wasan Manchester City, Jerome Boateng aikin tiyata a gwiwarsa bayan raunin daya samu a lokacin da yake takawa Jamus leda.

Boateng ya samu raunin ne a lokacin dayake motsa jiki, kafin wasan share fage da Jamus ta buga da Kazakhstan.

Dan wasan mai shekaru haihuwa 22 ya koma Manchester City ne a ranar litinin domin ayi mishi aikin tiyata.

Raunin daya samu ya zama babban koma baya ga yunkurin da Manchester City ke yi na samu gurbin taka leda a gasar zakarun Turai a badi bayan da shima Micah Richards ya samu rauni a cinyarsa.