Andy Murray ya sallami kocinsa

Image caption Andy Murray

Dan wasan Tennis din Burtaniya Andy Murray ya sallami kocinsa Alex Corretja.

Corretja, yana aiki ne da Andy Murray na wucin gadi tun daga watan Afrailun shekarar 2008.

A lokacin da kocin ke tare da Murray, dan wasan tenis din ya buga wasan karshe a gasar cin kyautar grand slam sau uku, sannan kuma ya lashe kyautar Grand Slam series sau shida.

Rahotanni na nuni da cewa Murray zai nada tsohon dan wasan Tennis Ivan Lendl a matsayin kocinsa.

A ranar juma'ar da ta gabata ne dai Alex Bogomolov ya fidda Murray a zagaye na uku a gasar Sony Ericsson Open.