An gano wanda ya jefi Neymar da ayaba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Neymar

Wani matashi dan Jamus ya ce shine ya jefi dan wasan Brazil Neymar da ayaba a filin wasan na Emirates.

Neymar ya zargi magoya bayan Scotland da yi mishi ihu da kuma kalamu babancin launin fata a wasan sada zumuntar da Brazil ta doke Scotland da ci biyu da nema.

Hukumar kwallon Scotland dao ta musanta zargin da dan wasan ya yi.

Kungiyar Arsenal ta da hukumar 'yansanda a Ingila sun gudanar da bincike kan al'amarin a yayinda wani dan Jamus ya amicewa cewar shine ya jefi dan wasan da ayaba.