Uche yana murnar dawowa murza tamoula

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Najeriya, Ikechukwu Uche

Dan wasan Najeriya, Ikechukwu Uche ya ce ya yi matukar murna da zuera kwallaye biyu bayan ya dawo takawa Najeriya leda a yayinda ya gama jinyar rauni na tsawon watanni 18.

Dan wasan wanda harwayau yake takawa kungiyar The Real Zaragoza leda ya shigo ne daga benci a wasan da Super Eagles ta lallasa Ethopia da ci hudu da nema a Abuja.

Nasarar da Najeriyar ta samu ya sa ta zama ta biyu a rukunin B a wasan share fage na taka leda a gasar cin kofin kasashen Afrika wanda za'a shirya a shekarar 2012.

"Ina matukar murna bayan wani dogon zango, ba san zan iya dawowa in taimaka kasa ta ba." In ji Uche a hirarsa da BBC.