Za mu siyo sabbin matasan 'yan kwallo-Ferguson

ferie Hakkin mallakar hoto
Image caption Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson na saran siyo sabbin 'yan kwallo biyu ko uku a sabuwar kakar wasa mai zuwa,inda ya ce masu kulob sun bada gudunmuwa ta wannan fannin.

Amma a cewar kocin, za a kashe kudadenne wajen siyo matasan 'yan kwallo da zasu karawa tawagar karfi,amma ba za a siyo gogaggun 'yan kwallon ba.

Da yake jawabi ga manema labarai, Ferguson ya ce "muna tunanin wasu sabbin 'yan kwallo biyu ko uku".

Ya kara da cewar"muna jin dadin matasan 'yan kwallo, saboda a baya muna kawo Cristiano Ronaldo da Wayne Rooney da Javier Hernandez".

A halin yanzu Manchester United na kokarin lashe kofina uku a kakar wasa ta bana, inda take jiran wasan zagayen kusada karshe a gasar cin kofin FA, da kuma wasan zagayen gabda na kusada karshe a gasar zakarun Turai tsakaninta da Chelsea a yayinda kuma take jan ragama akan teburin gasar premier.

A shekarar 1999, Manchester United ta lashe kofin uku karkashin jagorancin Sir Alex Ferguson.