Kotu ta haramta yajin aiki a gasar La Liga

messi
Image caption Zaratan gasar La Liga

Za a buga gasar La Liga ta Spaniya kamar yadda aka tsara a karshen mako, bayan da wata kotu a Madrid ta amince da kalabalantar da wasu kungiyoyi shida suka shigar akan batun shirin yajin aiki.

Kungiyar dake kula da gasar kulob kulob ta yi kira a dakatar da gasar don nuna rashin jin dadibsy akan batun nuna wasa daya a kowanne mako a kyuata a gidajen talabijin.

Amma kungiyoyi kamarsu Sevilla da Villarreal sun shigar da kara don kalubalantar matakin.

Daa anyi yajin aikin, to da an tsawauta gasar La Liga da makwanni uku.

Amma hukuncin kotun na nufin cewar Real Madrid zata fuskanci Sporting Gijon a ranar Asabar, kwanaki uku kafon wasan gasar zakarun tsakaninta da Tottenham.

Hukumar kwallon kwararru na Spaniya ta sanarda yinkurinta na yajin aiki a watan Fabarairi don dakatar da dokar yada labarai ta shekarar 1997.