Lucas Leiva ya sabunta kwangilarshi a Liverpool

Lucas Leiva
Image caption Lucas Leiva ya tare kwallo da kai

Dan Brazil wanda ke taka leda a Liverpool Lucas Leiva ya sabunta yarjejeniyarshi don shafe lokaci mai tsawo a kulob din.

Dan wasan mai shekaru 24 ya koma Anfield ne a shekara ta 2007 daga Gremio akan pan miliyan biyar.

Lucas shike lura da tsakiyar Liverpool bayan tafiyar Xabi Alonso da Javier Mascherano, kuma a watan Fabarairu ya buga wasanshi na 100 a Anfield.

Kocinsa Kenny Dalglish yace:"tun zuwa na kungiyar, ya kasance dan wasan da muke ji dashi".

Lucas ya bugawa kulob din wasanni 40 a kakar wasa ta bana, kuma ya buga wasan Brazil da Scotland a filin Emirates a ranar Lahadi.

Darekta dake kula da kwallon kafa a Liverpool Damien Comolli shine ya jagoranci sasantawa akan batun kwangilar.