2012:Tottenham ta kai karar shugaban Olympics

olym[pics Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Filin wasan da ake fada tsakanin West Ham da Spurs

Kungiyar Tottenham Hotspur ta kai karar shugaban kwamitin olympics kotu akan hukuncin baiwa kungiyar West Ham filin wasa bayan kammala gasar a 2012.

Kamfanin Olympic Park Legacy Company (OPLC) wanda ya zabi West Ham a watan daya gabata, kuma kamfanin ya tabbatar da cewa Tottenham na kokarin daukar matakin kuliya.

Tottenham ta bayyanawa OPLC shawarar data yanke ne a wannan makon, bayan kamalla filin wasan na Olympics.

Kakakin magajin garin London ya kare matakin yadda aka zabi kungiyar da zata karbi filin wasan.

Tottenham na kalubalantar yadda OPLC ta zabi West Ham don karbe ikon filin wasan bayan kamalla gasar Olympics na badi.