Raunin Robin Van Persie baida tsanani-Marwijk

persie
Image caption Robin van Persie da kocinsa Bert van Marwijk

Kocin Netherlands Bert van Marwijk ya ce raunin da Robin van Persie yaji ba mai tsanani bane.

Dan kwallon Arsenal din shine ya fara zira kwallo a wasan da Netherlands ta lallasa Hungary daci biyar da uku amma sai ya jimu kafin a fara wasan, abinda ya tilasta aka fiddashi a wasan.

An yi tunanin cewar dan wasan zai shafe lokaci mai tsawo baya taka leda saboda rauni, amma mai horadda 'yan kwallon ya ce baya tunanin zai dade yana jinya.

Van Marwijk ya shaidawa manema labari cewar:"bana tunanin raunin mai tsanani ne duk da cewar yana damuwa a gwiwarshi".

Van Persie ya shafe lokaci mai tsawo yana jinya a Arsenal kuma a kwananan ne ya nuna damuwa akan gwiwarshi bayan wasansu da Birmingham.