Ana bukatar karin bakaken fata a matsayin koci

ince Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Paul Ince

Ministan wasannin Birtaniya Hugh Robertson ya kalubalanci hukumar dake kula da kwallon Ingila FA akan cewar ta gaza wajen baiwa bakaken fata 'yan Ingila dama a matsayin 'yan wasa da kuma masu horadda 'yan wasa.

A cewar Robertson ya kamata FA ta dauki matakin da ya dace da magance matsalar kamar yadda wasu bangarorin wasanni suka yi.

A halin yanzu Paul Ince na Notts County da kuma Chris Powell na Charlton Athletic sune kadai masu horadda 'yan kwallo biyu cikin kulob 92 na Ingila.

Shugaban kungiyar kwararrun 'yan kwallo a Ingila Gordon Taylor ya ce zai bada goyon baya wajen kawo karshen wannan batun na nuna bambamci.

A cewar Taylor zai goyi bayan kafa sabuwar doka kamar yadda yake wajen gudanar wasan kwallon kankara na Amurka.

Ince ya kasance bakin bature na farko daya jagoranci kulob a gasar premier lokacin daya koma Blackburn Rovers a watan Yunin 2008.

Amma sai aka sallameshi bayan watanni shida a Rovers inda kulob din ya samu nasara a wasanni uku cikin 17.