Siasia 'nada kananan maganganu'-Odemwingie

Osaze Odemwingie
Image caption Osaze Odemwingie

Dan kwallon Najeriya Osaze Odemwingie a shafinsa na sada zumunci na Twitter ya zargi kocinsa Samson Siasia akan cewar 'yana da kananan maganganu'.

Odemwingie ya fusata akan cewar ana tuhumar matakin daya dauka na kin shiga wasan sada zumunci na Super Eagles tsakaninta da Kenya a ranar Talata.

Bayan ya buga wasan Najeriya da Ethiopia na neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika a badi a ranar Lahadi, sai ya koma Ingila a ranar Litinin.

Odemwingie a shafinsa na Twitter cewar rauni ne ya hanashi tsayawa ya buga wasan.

A cewar shi"jin cewar Siasia na fushi dani saboda na tafi, ina ganin ya kamata ya kara tunani".