An sake dage zaben 'yan Majalisa a Najeriya

breaking
Image caption Shugaban INEC Attahiru Jega na fuskantar babban kalubale

A karo na biyu hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya wato INEC ta dage zaben 'yan majalissun dokokin kasar.

A cewar hukumar INEC za a gudanar da zabenne a ranar tara ga watan Afrilu sabannin ranar Litinin hudu ga watan Afrilu data sanar a baya.

Tun farko ranar Asabar biyu ga wata ne aka shirya zaben amma sai INEC ta dakatar jim kadan da farawa saboda rashin isar kayayyakin zabe a wasu sassan kasar akan lokaci.

Dama dai, gamayyar jam'iyyun adawa a Najeriya sun nuna rashin amincewarsu akan gudanar da zaben 'yan majalissun a ranar Litinin bisa fargabar cewar yayi kusa.

Zaben 'yan majalissun dokoki- Tara ga watan Afrilu.

Zaben shugaban kasa-16 ga watan Afrilu.

Zaben gwamnoni da 'yan majalissun dokoki- 26 ga watan Afrilu.