Bamu fidda ran lashe gasar premier ba-Ancelotti

premeir
Image caption Tambarin gasar premier

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya hakikance ba zasu fidda rai akan lashe gasar premeir ba duk da cewar Manchester United wacce ke jan ragama, inda ta dara Chelsea da maki goma sha daya.

Chelsea wacce ta lashe gasar premier a kakar wasan data wuce, ta tashi kunen doki ne tsakaninsu da Stoke a ranar Asabar, abinda ke nufin cewar kungiyar da kamar yuwa ta lashe gasar premier ta bana.

Sakamakon wasu karawar premier:

*West Ham United 2 - 4 Manchester United *Birmingham City 2 - 1 Bolton Wanderers *Everton 2 - 2 Aston Villa *Newcastle United 4 - 1 Wolves *Stoke City 1 - 1 Chelsea *West Brom 2 - 1 Liverpool *Wigan Athletic 0 - 0 Tottenham Hotspur *Arsenal 0 - 0 Blackburn Rovers *Fulham 3- 0 Blackpool