Masar ta nemi afuwar Tunisia akan kaiwa 'yan wasa hari

zamalek Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Magoya bayan Zamalek

Firayi Ministan Masar Essam Sharaf ya nemi afuwar Tunisia saboda magoya bayan Zamalek cikin fushi sun shiga filin wasa suka kaiwa 'yan kwallon Club Africain hari a birnin Alkahira a ranar Asabar.

Sharaf ya umurci ministan harkokin cikin kasar ya gudanar da bincike akan lamarin.

Shiga filin ya tilasta dakatar da wasan na gasar zakarun Afrika tsakanin Zamalek da Club Africain.

Magoya bayan Zamalek sun fusata ne suka shigo fili bayan alkalin wasa ya hana wata kwallo data shiga raga akan cewar dan Zamalek yayi satan gola.

Sun kaiwa alkalin wasa hari da kuma 'yan kwallon Tunisia lamarin da aka nuna kai tsaye a gidajen talabijin.

A lokacin wasan dai Zamalek nada ci biyu sai Club Africain nada ci daya, sannan a bugun farko Zamalek ta sha kashi daci hudu da biyu.