Bale zai buga wasanmu da Real Madrid-Redknapp

bale
Image caption Gareth Bale da Van der vaat

Kocin Tottenham Harry Redknapp yace akwai yiwuwar Gareth Bale zai buga wasansu na gasar zakarun Turai tsakaninsu da Real Madrid a ranar Talata.

Bale yayi fama da rauni a 'yan makwannin nan amma Redknapp na saran dan kwallon Wales din zai taka leda a Madrid.

Redknapp yace"ina da kwarin gwiwa akan Gareth, idan ace ya buga wasanmu da Wigan, da ya kara turgudewa, amma tun da ya huta, akwai alamun zai shiryawa Real Madrid".

Bale wanda wasa uku kacal ya buga minti casa'in a gasar premier ta bana, ba shi kadai bane damuwar Spurs, saboda William Gallas na fama da rauni a kafadarshi.

Haka zalika Steven Pienaar ba zai buga wasan ba saboda rauni.

Bugu da kari wasu 'yan wasan Spurs dake fama da rauni sune Alan Hutton da Ledley King da Younes Kaboul da kuma Jonathan Woodgate.

A bangaren Real Madrid kuwa akwai tababa akan lafiyar Cristiano Ronaldo da Karim Benzema da Marcelo a yayinda ake saran Gonzalo Higuain zai buga.