Bin Hammam ne kawai za kalubalanci Blatter

Mohamed Bin Hammam
Image caption Mohamed Bin Hammam ya bayyana aniyarsa ne a watan Maris

A yanzu ta tabbata cewa Mohamed Bin Hammam ne kawai zai fafata da Sepp Blatter a zaben shugabancin Hukumar Kwallon kafa ta duniya FIFA a ranar 1 ga watan Juni.

Shugaban Hukumar Kwallon kafa ta Asia, mai shekaru 61, ya bayyana aniyarsa ta tunkarar Blatter ne mai shekaru 75, a watan Maris din da ya gabata.

Tun shekarar 1998, Blatter ya ke shugabantar Hukumar FIFA, amma ya yi alkawarin idan aka zabe shi a karo na hudu, to zai sauka idan wa'adinsa ya kare a shekara ta 2015.

Za a zabi shugaban na FIFA ne a babban taron Hukumar wanda za a fara a ranar 31 ga watan Mayu.

Ranar 1 ga watan Afrilu aka ware domin tabbatar da 'yan takara kuma 'yan takarar na bukatar kashi biyu bisa uku na kuri'un a matakin farko, ko kuma rinjaye kai tsaye a mataki na biyu.

Bin Hammam shi ne mutum na farko da zai kalubalanci Blatter, tun bayan da shugaban Hukumar Kwallon kafa ta Afrika Issa Hayatou ya kalubalance shi - sannan ya fadi da kuri'u 139 da kuma 56 a shekara ta 2002.