Iran ta nada Queiroz a matsayin koci

queiroz
Image caption Carlos Queiroz ne ya kai Portugal gasar 2010

Tsohon kocin Portugal Carlos Queiroz ya kulla yarjejeniya da Iran don horadda 'yan kwallonta daga nan zuwa karshe gasar cin kofin duniya a shekara ta 2014.

A cewar hukumar dake kula da kwallon Iran, za a dunga biyan Queiroz dala miliyan biyu a duk shekara.

Rahotanni sun nuna cewar kocin ya isa birnin Tehran a ranar Litinin inda yace zai taimakawa kasar ta samu gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a buga a Brazil a shekara ta 2014.

Quieroz ya ce "lokaci yayi da zamu hada kan gogaggun 'yan wasa ta yadda zamu samu nasara".

Quieroz ya maye gurbin Afshin Ghotbi wanda aka ki sabunta kwangilarshi sakamakon fidda Iran a gasar cin kofin kasashen nahiyar Asiya a farkon bana.

Dan shekaru hamsin da bakwai, tsohon kocin Real Madrid dinne ya jagoranci Portugal zuwa gasar cin kofin duniya da aka yi a Afrika ta Kudu a shekara ta 2010.