Watakila FA ta dakatar da Rooney na wasanni biyu

rooney Hakkin mallakar hoto b
Image caption Watakila Rooney ba zai buga wasansu da City ba

Hukumar dake kula da kwallon Ingila wato FA zata iya dakatar da Wayne Rooney na wasanni biyu saboda amfani da kalaman da basu daje ba a wasan da United ta casa West Ham daci hudu da biyu.

Dan wasan bayan da ya zira kwallo ta uku sai yayi wasu kamalai a gaban na'urar daukar hoto a Upton Park.

Daga nan zuwa karfe shida na ranar Talata, Rooney keda damar daukaka kara akan tuhumar.

Idan har bai kare kanshi ba, za a dakatar dashi na wasanni biyu, amma idan ya musanta za a saurari karar a ranar Laraba.

Idan aka dakatar dashi na wasa guda, Rooney ba zai buga wasansu da Fulham ba, idan kuma dakatarwar ta wasanni biyu ce, to ba zai buga wasansu da Manchester City ba na kofin FA.

Nan take dai a ranar Rooney ya nemi afuwa akan abinda yayi, bayan nasarar ta baiwa United damar samun tazarar maki bakwai akan teburin gasar premier.