West Ham na bincike akan wulakanta dan uwan Obinna

west ham
Image caption West Ham

Kungiyar West Ham na bincike akan rahoton cewar an nunawa iyalan 'yan wasanta biyu wayiwar launin fata wato Victor Obinna da Frederic Piquionne bayan Manchester United ta doke kulob din a ranar Asabar.

Obinna dan Najeriya da Piquionne dan New Caledonia an shigo dasu ne bayan hutun rabin lokaci a wasan da aka buga a Upton Park.

Kungiyar na duba hutunan bidiyo kuma tana tattaunawa da shaidu, inda ta ce duk wanda aka kama da laifi, tabbas za a hukunta shi.

Shugaban West Ham David Sullivan ya bayyanawa jaridar Evening Standard cewar zasu tabbatar da gaskiya akan zargin.

Ya kara da cewar "duka mutane dai dai suke, an haife mu da baiwa daban daban".

Rahotanni sun nuna cewar wani dan uwan Obinna ya kalli wasan inda aka kebewa manyan baki daga bisani sai wasu 'yan kallo suka nuna mashi kyama.