U 20: Caf ta sanarda Johannesburg a madadin Tripoli

caf
Image caption Tambarin CAF

Hukumar dake kula da kwallon Afrika wato CAF ta sanar cewa za ayi gasar kwallon matasan nahiyar 'yan kasada shekaru ashirin a birnin Johannesburg.

An maida gasar zuwa Afrika ta Kudu ne a watan daya gabata sakamakon tashin hankalin da ake yi a Libya, kasar da yakamata ta dauki bakuncin gasar.

Kasashe takwas ne zasu fafata a gasar da za a fara a ranar 17 ga watan Afrilu zuwa daya ga watan Mayu.

Afrika ta Kudu wacce ta maye gurbin Libya, na rukunin farko ne tare da Mali da Lesotho da Masar.

Rukuni na biyu na kunshe ne da kasashen Ghana, Kamaru, Najeriya da kuma Gambia.

Kasashen da suka tsallake zuwa zagayen kusada karshe ne zasu wakilci Afrika a gasar cin kofin duniya da za ayi a Columbia a watan Yuli zuwa Agusta.