An fidda sabon tsarin zabe a kwallon Kenya

kenya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan kwallon kulob na Kenya

Za ayi amfani da sabon tsari wajen zaben sabon shugaban hukumar kwallon Kenya, a wani matakin murkushe cin da hanci da rashawa.

A karon farko duka kulob din kasar kusan su 3000 zasu kada kuri'a.

A baya wasu wakilan shiyoyi ne da ake nadawa suke zaben.

A cewar shugaban hukumar zaben Kenya Peter Ogonji "tsarin da ake bi a baya na bada damar zaben shugabannin da basu dace ba wadanda suke sayen kuri'un".

A wannan watan za a gudanar da zaben shugabannin hukumar kwallon Kenya.

Ana saran sabon zaben zai kawo karshen shekarun da aka shafe ana takadama akan harkokin kwallon Kenya da yaki ci yaki cinyewa.