Gasar Bundesliga na fuskantar koma baya-Loew

loew
Image caption kocin Jamus Joachim Loew

Kocin Jamus Joachim Loew ya bayyana cewar gasar Bundesliga tana fuskantar koma baya inda aka kwantata da gasar Ingila da Spaniya.

A cewar Loew kungiyar daya tal wato Schalke 04 ce ke zagayen gabda na kusada karshe a gasar zakarun Turai sabanin Ingila da Spain masu wakilci da yawa.

Loew yace"wannan lamarin bai nuna cewar ana murza leda da kyau a Bundesliga ba".

A halin yanzu Jamus bata da wakilci a gasar Europa.

Ingila nada kungiyoyi uku dake wakiltar ta a gasar zakarun Turai wato Tottenham da Chelsea da kuma Manchester United.

Sai kuma Spain wacce Barcelona da Real Madrid ke wakilta a wannan matakin na gasar.

Loew ya kara da cewar"a halin yanzu Bundesliga na fuskantar matsala".

Akalla kungiyoyi 12 cikin 18 na gasar Bundesliga sun riga sun canza masu horadda 'yan kwallonsu ko kuma sun sanarda cewa zasu sallami kocin a karshen kakar wasa ta bana.