Obinna ya karyata batun wulakanta 'yan uwanshi

obinna
Image caption Victor Obinna Nsofor

Dan kwallon West Ham Victor Obinna Nsofor ya karyata rahotannin dake cewar an nunawa 'yan uwanshi wariyar launin daga wajen magoya bayan kulob din a ranar Asabar data wuce.

Kungiyar ta bada sanarwar soma bincike akan batun bayan Manchester United ta casa Hammers din daci hudu da biyu.

Amma dan kwallon ya shaidawa BBC cewar yaji mamaki akan lamarin da bai taba aukuwa ba.

Obinna yace"babu abinda ya faru, saboda babu wani dan uwana a Ingila".

Ya kara da cewar " babu wata hujjar tambaya ta in tabbatar da lamarin tunda bai faru ba".

Rahotanni sun nuna cewar West Ham na bincike akan batun nuna wariyar launin fata akan 'yan uwan Obinna da kuma na Frederic Piquionne.