Chelsea ta fi mu dama - Vidic

Nemanja Vidic Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Nemanja Vidic shi ne yake sawa United kyaftin a 'yan kwanakin nan

Dan wasan Manchester United Nemanja Vidic ya ce nasarorin da Chelsea ta samu a kan United a baya-bayan nan, ya sa tafi United din dama a wasan da za su kara a gasar zakarun Turai.

United za ta yi tattaki zuwa Stamford Bridge a ranar Laraba a zagayen farko na wasan dab da na kusa da na karshe, kuma shekaru tara kenan rabon da ta yi nasara kan Chelsea a Stamford Bridge.

"Suna da dama, saboda sun samu nasarori a kan mu," a cewar Vidic.

"Amma wannan gasar zakarun Turai ce, abinda ya fi shi ne mu samu mu zira kwallo."

Vidic zai fafata da Fernando Torres, wanda ya saba wahalar da shi a lokacin da yake Liverpool, sai dai har yanzu bai zira kwallo a Chelsea ba, tun bayan da suka saye kan fan miliyan 50.