Ina son in cigaba da taka leda a Bernabeu-Adebayor

Emmanuel Adebayor Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Emmanuel Adebayor da Mourinho

Emmanuel Adebayor ya ce yanasaran kwallaye biyun daya zira a wasan da Real Madrid ta casa Tottenham Hotspur zasu taimaka ya cigaba da kasancewa a Bernabeu na lokaci mai tsawo.

Dan kwallon Togon ya ci kwallayen ne a wasan zagayen gabda na kusada karshe da suka buga a Madrid.

Adebayor ya ci kwallaye biyar cikin wasanni 13 tun zuwanshi Real Madrid a matsayin aro daga Manchester City.

Yace"Ina da sauran watanni biyu in tafi,kuma kungiyar ce zata yanke hukunci akan ko tanason in tafi ko in zauna".

Kocin Madrid Jose Mourinho ya kawo Adebayor zuwa Bernabeu saboda raunin da Gonzalo Higuain ya samu.

A ranar Laraba 13 ga watan Afrilu za ayi bugu na biyu tsakanin Real da Spurs, kuma duk kungiyar data samu nasara zata hadu kulob din daya samu nasara a wasa tsakanin Barcelona da Shakhtar Donetsk.